Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya aike da sakon ta’aziyya ga Gwamnan jihar Kano

0 72

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya aike da sakon taaziyya ga takwaransa na jihar Kano bisa rasuwar wasu muhimman mutane biyu a jihar da suka hadar da shugaban jamiyyar PRP na kasa Farfesa Sule Bello da kuma wani sanannan dan siyasa Farfesa AD


Sakon ta’aziyyar mai dauke da sa hannun mai baiwa gwamna shawara kan kafafan yada labarai da Hulda da jama-a Habibu Nuhu Kila, Gwamnan ya bayyana rasuwar mutanen biyu a matsayin babban rashi ga jama’ar jihar Kano da kuma kasa baki daya.


Yace za’a dade ana tunawa da yan siyasar biyu bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen cigaban jihar da kasa baki daya.
Daga nan sai gwamnan ya yi adduar Allah ya jikansu ya kuma baiwa iyalai da yan uwa hakurin jure babban rashin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: