Gwamna Namadi ya ƙaddamar da rabon tallafin Kuɗi ₦1,080,000,000 ga al’ummar ƙananan hukumomin jihar Jigawa

0 348

Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar A. Namadi FCA ya ƙaddamar da Tallafin Kuɗi Naira Biliyan ɗaya da Miliyan Tamanin (1,080,000,000) wan da za a rabawa al’umma a ƙanana Hukumomo 27 dake faɗin Jihar Jigawa da Kuma kayan abinci da suka tasamma Sama da Naira Biliyan Biyu (2 Billion).

Gwamna Namadi ya ƙaddamar da kayan a Ƙaramar Hukumar Gumel a madadin yanda zai gudana a dukkan ƙananan hukumomin.

Tallafin ya haɗa da Buhun Shinkafa Dubu Arba’in da Bakwai da Ɗari Huɗu da Goma Sha Biyu (47,412) da Katon ɗin Taliya Dubu Talatin da Uku da Ɗari Biyu da Ashirin da Tara(33229) da Kuma Masara Dubu Takwas da Ɗari Uku (8300) da kuma mutum Dubu Huɗu (4000)da za a bawa nai Dubu Goma (10,000) a kowacce ƙaramar Hukuma da ya kama Mutane Dubu Ɗari da takwas (108,000) a faɗin Jihar ne zasu amfana da tallafin kuɗin.

Gwamnan ya tabbatarwa da al’umma cewa” A matsayin Gwamnati zamu yi bakin ƙoƙarinmu wajen ganin mun fitar da al’umma daga halin da suke ciki na matsi kuma insha Allahu wannan somin taɓi ne akan abubuwan da muka saka gaba nan gaba kaɗan zasu tabbata”

Leave a Reply

%d bloggers like this: