Gwamna Namadi ya mika ta’aziyyarsa ga Gwamnatin Kano bisa mutuwar ‘Yan wasa 22 sanadiyyar haɗarin mota
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya mika ta’aziyyarsa ga Gwamnati da al’ummar Jihar Kano dangane da haɗarin mota mai muni da ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan wasa 22, masu horarwa da jami’an wasanni na jihar, waɗanda suke kan hanyarsu ta dawowa daga Gasar Kasa ta Wasannin (National Sports Festival) da aka gudanar a Jihar Ogun.
Gwamnan ya ce shi da gwamnati da mutanen Jigawa sun yi matuƙar bakin ciki da wannan lamari mai ciwo.
A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Hamisu Gumel, ya aikewa da sako daga wurin Malam Namadi, an jaddada cewa:
Wannan mummunan abin da ya faru a gadar Chiromawa da ke kan titin Kano-Zaria a ranar Asabar, ya sanya zukata cike da baƙin ciki.
Gwamna Malam Umar Namadi na mika ta’aziyya ta ƙwarai ga Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf, Gwamnatin Jihar Kano, iyalan mamatan, da dukkan al’ummar wasanni a fadin kasar nan.