Gwamna Namadi ya rantsar da kwamittin hukumar kula da tsaftar muhalli a jihar Jigawa

0 257

Gwaman jihar Jigawa Mallam Umar Namadi, ya rantsar da kwamittin hukumar kula da tsaftar muhalli ta na jiha wanda zai sanya ido kan tsaftace dukkanin muhalli a jihar.

Kwamishinan muhalli na jiha Dr. Nura Ibrahim shi ne zai jagoranci kula da kwamittin.

Kwamitin ya kunshi wakilan masu rike da sarautar gargajiya da hukumomin tsaro da masana da kuma kungiyoyin al’umma.

Mallam Umar Namadi, yace kwamittin an dora masa alhakin kula da tsaftar muhalli a dukkanin fadin jihar.

Idan dai za a iya tunawa wannan kwamitiin na daya daga cikin kudurin gwamnatinsa daga cikin manufofi 12 da gwamnan yace zai mayar da hankali akan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: