Gwamna Nasir El-Rufai ya ce rahoton bincike ya alakanta wasu jami’an ‘yan sanda da sojoji da ke aiki tare da ‘yan bindiga

0 42

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce rahoton bincike ya alakanta wasu jami’an ‘yan sanda da sojoji da ke aiki tare da ‘yan bindiga.

Gwamnan ya ce da gwamnati za ta iya katse hanyoyin samun kudaden ‘yan bindigar da kuma dakile hanyoyin samar da kayayyaki, da an samu nasarar kashi 50 cikin 100 a yakin.

A wani batun kuma, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya ce ba shi da burin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023, inda ya yi alkawarin marawa duk wani dan takarar shugaban kasa da ya fito daga kowace shiyya a kudu.

Gwamnan ya bayyana haka ne a jiya a lokacin da yake gabatar da tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban kasa yayin taron tattaunawa na mako-mako da kungiyar kafafen yada labaran fadar shugaban kasa ta shirya a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Nasir El-Rufai, wanda shi ma ya bayyana fatansa na samun wanda zai gaje shi daga cikin mutanensa, ya ce a karshe al’ummar jihar Kaduna ne zasu yanke hukunci saboda ba zai iya nuna kowa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: