Gwamna Nasir El-Rufai ya hana karbar kudin daliban makarantun sikandire a jihar Kaduna

0 82

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya ce tsarin biyan kudin makaranta ga daliban sakandiren jihar da ma’aikatar ilimin jihar ta bullo da shi ya ci karo da tsare-tsaren Gwamnatin Jihar.

Gwamnatin ta umarci Shugabannin Makarantun su dawo da kudaden suka karbi ga Daliban cikin gaggawa.

Majalisar Zartarwar Jihar Kaduna, a zaman da ta gudanar na ranar Litinin, ta sake Jaddada kudurin Gwamnatin Jihar na yin karatu Kyauta a Jihar har tsawon shekaru 12.

A baya dai Ma’aikatar ilimin Jihar ta fitar da sanarwar da ke cewa daliban sakandire a jihar za su fara biyan kudin makaranta.

Sai dai Cikin wata sanarwa da Mataimakin Gwamnan na musamman kan harkokin Yada Labarai Mista Muyiwa Adekeye ya sanya wa hannu gwamnan ya bayyana tsarin ilimi kyauta a matsayin babban burin da gwamnatinsa ta sanya a gaba.

Sanarwar ta ce Gwamatin Jihar za ta ci gaba da aiwatar da tsarin ilimi kyauta ga daliban sakandire a fadin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: