Gwamna Nasir El Rufa’i na jihar Kaduna ya tabbatar da kasancewar ‘yan ta’addar Ansaru da sauran miyagun mutane a jihar.

Nasir El-Rufa’i ya bayyana hakan ne a jiya a yayin taron majalisar tsaro na jihar inda ya saurari bayanai daga kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan.

A cewar gwamnan, karuwar ‘yan ta’addar Ansaru da na Boko Haram a jihar da kuma yadda suke mu’amala da ‘yan fashin daji ne ya haddasa harin da aka kai kan hanyar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris inda har yanzu fasinjojin da aka yi garkuwa da suke tsare.

Ya kara da cewa ‘yan ta’addan na tasowa daga yankin Arewa maso Gabas zuwa Arewa maso Yamma, kuma a yanzu haka suna shigar da matasa cikinsu.

Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ya damu da yadda ‘yan ta’adda ke amfani da bama-bamai tare da yin kira da a kafa sansanin aiki na sojoji a yankin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: