Gwamna Zulum ya bayyana abubuwan da aka gano kan jarrabar da aka yi wa malaman firamare a jihar Borno

0 110

Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya bayyana abubuwan da aka gano a rahoton da aka mika masa kan jarrabar da aka yi wa malaman firamare na jihar da cewa abin tsoro ne matuka.

Farfesa Zulum ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis bayan da kwamitin da aka dora wa aikin yi wa malaman firamaren Dubu 17,229 na kananan hukumomin jihar 27 Jarrabawar rubutu da karatu da kuma lissafi.

Kwamishinan Ilimi na jihar, Lawan Abba Wakilbe, shi ne ya gabatar da rahoton.

Binciken ya gano cewa daga cikin malaman Dubu 17,229 a fadin jihar kashi 31.6 cikin dari ne kawai suka cancanci koyarwa.

Malamai Dubu 3,815, kashi 22.1 cikin dari ba su cancanci koyarwa ba kuma ma ba za a iya musu horo su iya aikin ba, kamar yadda rahoton ya nuna.

Sai dai gwamnan na Jihar Borno ya bayar da tabbacin cewa duk da matsalolin da aka gano ba zai kori wadanda ba za su iya koyarwar ba, amma bisa shawarar kwamitin zai duba yuwuwar mayar da su wuraren da za su iya wasu ayyukan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: