Gwamna Zulum ya dakatar da dukkanin shugabannin kwalejin kimiyya ta Ramat na tsawon watanni shida

0 102

A dai jihar ta Borno, Gwamna Babagana Zulum ya dakatar da dukkanin shugabannin kwalejin kimiyya ta Ramat Polytechnic da ke birnin Maiduguri, na tsawon watanni shida.

Gwamna Zulum ya kasance dalibin kwalejin daga shekarar 1986 zuwa 1988.

Ya sami takardar difloma a fannin Injiniyan Noma kafin ya koma Kwalejin a matsayin shugabanta daga shekarar 2011 zuwa 2015.

A yayin ziyarar ta ba zata, gwamnan ya kadu matuka da ganin yadda guraren koyon aiki da dakunan gwaje-gwaje ba sa aiki.

Gwamnan ya ziyarci kwalejin da misalin karfe 9 na safe inda ya iske yawancin dakunan gwaje-gwajen sun dena aiki, wasu kuma yana ta mamaye su da beraye na yawo saboda rashin kulawa.

Bayan zagayawa kwalejin da duba komai, Gwamna Zulum ya umarci kwamishinan ilimi mai zurfi, kimiyya, fasaha da kere-kere na jihar, Dakta Babagana Mallumbe, da ya kula da gudanar da kwalejin, ba tare da bata lokaci ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: