Gwamna Zulum ya raba wa likitoci fiye da 80 didaje da kudi Naira miliyan 79 don inganta rayuwarsu

0 78

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara  Zulum, ya mika rukunin gidaje 81 tare da cakin Naira Miliyan 79 ga wasu likitocin jihar 81 don inganta rayuwarsu.

An bai wa likitocin gidaje masu dakunan kwana uku-uku, kewaye da katanga da kayayyakin alatu da shaguna biyu a rukunin gidajen mai dauke da filin wasa da sauransu.

Bangarori 13 da ke rukunin na dauke da gidaje 78 sai wani ginin bene da ke asibitin tunawa da Muhammadu Shuwa da ke da karin gidaje uku.

A halin yanzu dai biyu daga cikin gidajen 81 ne aka kammala, 79 kuma ba a kammala su ba a sabon rukunin gidajen ma’aikatan da aka kaddamar na likitocin jihar Borno.

Zulum ya kuma mika cekin Naira miliyan daya a matsayin tallafin kayan daki ga likitoci 79 da aka raba wa gidajen da ba a kammala gyara su ba, don su da kansu su samu damar kammala su da kansu.

Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar gidajen 81 shi ne Dokta Bulama Gaidam, wanda a halin yanzu ke hannun kungiyar ISWAP.

An sace Dokta Gaidam ne a ranar Laraba, 16 ga Maris, 2022 a Gubio, inda yake aiki a matsayin babban jami’in kula da lafiya na babban asibitin garin.

Da yake magana da matar likitan da aka sace, Zulum ya jajanta mata tare da karfafa gwiwar cewar wata rana za ta sake haduwa da mijinta cikin hukuncin Allah.

Gwamnan ya kuma ba da tabbaci cewa duk likitocin 81 da suka amfana gwamnati za ta tallafa wajen samar musu da injin janareta mai bada hasken wutar lantarki don sanyawa rukunin gidajen.

Sai dai ya bukace su da su kafa kungiyar mazauna yankin da za su iya ba da gudummawa ta hanyar nemo hanyoyin da za a ci gaba da kula da gidajen, da kuma inganta tsaron mazauna.

Zulum ya yi alkawarin cewa, za a tallafa wa karin likitocin da ba su cikin mutane 81 da suka ci gajiyar tallafin ta wasu hanyoyi a ci gaba da kokarin gwamnati na inganta jin dadin  likitoci don samar musu da ingantacciyar rayuwa.

Idan za a iya tunawa, Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya kaddamar da rukunin gidajen likitocin a ranar 24 ga watan Fabrairun 2022, inda bayan haka aka tsara yadda za a gudanar da rabawa likitocin da za su amfana.

Osinbajo ya kaddamar da gidajen ne yayin da ya ziyarci Maiduguri domin kaddamar da Asibitin Gwamnatin Tarayya.

A lokacin da yake mika gidajen ga likitocin, Gwamna Zulum, ya bayar da umarnin a samar da motocin bas guda biyu wadanda za su rika tsayawa dindindin a rukunin gidajen domin kai mazauna asibitoci domin kula da lafiyar al’umma yadda ya dace.

Da yake nuna godiyarsu wakilin likitocin ya yi alkawarin cewa za su maida biki ta hanyar inganta ayyukan jinyar marasa lafiya yadda ya dace a asibitocin jihar.

Asalin Bayanin:

https://aminiya.dailytrust.com/zulum-ya-bawa-wa-likitoci-81-rukunin-gidaje

Leave a Reply

%d bloggers like this: