Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, a yau yace ana fuskantar barazanar fari a jihar muddin manoma basu samu damar komawa gonakinsu ba.

Babagana Zulum ya shaidawa sashin Hausa na BBC cewa lamarin yayi muni matuka, kasancewar dubban yan gudun hijira da suka koma kauyukansu basu da abinci kuma baza su iya noma ba.

Babagana Zulum ya ce babu rashin tsaron da ya kai munin rashin abinci kuma matukar babu abinci, komai zai iya faruwa.

Ya kara da cewa a yanzu jihar Borno na fuskantar karancin abinci kuma yaran jihar basa zuwa makaranta.

Gwamnan yace kungiyoyi masu zaman kansu da ke bayar da tallafi, sun yi iya kokarinsu amma yanzu sun dena bayar da tallafin abinci saboda abin yayi musu yawa.

Babagana Zulum yace akwai bukatar mutane su koma kauyukansu suyi noma da kasuwanci.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: