Gwamnan Badaru ya musanta cewa Tinubu zai zama shugaban kasar kudancin Najeriya ne kadai idan ya ci zabe

0 103

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar, ya musanta rade-radin da ake yi cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC zai zama shugaban kasar kudancin kasarnan idan ya ci zabe.

Gwamnan yayi ikirarin cewa abubuwan da dan takarar shugaban kasar ya aiwatar a baya sun nuna cewa ba mai cin amana ne ba.

Badaru Abubakar wanda yayi magana a Kano yayin zaman ganawa tsakanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da malaman addinin Musulunci daga Arewa maso Yammacin kasarnan yace dukkan abubuwan da Bola Tinubu ya aiwatar a baya sun bayyana a fili cewa ba mai nuna banbancin kabila ko addini ba ne.

Gwamnan na jihar Jigawa ya kara da cewa dukkan abubuwan da Bola Tinubu ya aiwatar yayin neman takararsa ta shugaban kasa, ya aiwatar ne bisa radin kashin kansa da Gwamna Abdullahi Ganduje da kuma Nuhu Ribadu, mutanen da aka san su da kishin kasa gabadaya.

Badaru Abubakar wanda yayi tilawar abubuwan da suka faru a baya akan yadda malaman addini suka matsa masa ya janye takararsa ta shugaban kasa domin dan takara daga kudu, yace dukkan masu kishin Najeriya ne suka yanke shawarar marawa Bola Tinubu baya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: