Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana damuwa bisa karuwar cin zarafin mata, musamman fyade a jihar, inda yayi alkawarin sanya dandaka a cikin sabuwar dokar cin zarafin bil’adama wacce ya sanyawa hannu kwanannan.
Bala Mohammed ya fadi haka lokacin da ya karbi bakuncin ministar harkokin mata da cigaban yara, Pauline Tallen, wacce ta kai masa ziyarar aiki jiya a gidan gwamnati dake Bauchi.
- Hisba ta kai samame wasu gidajen sayar da barasa uku a jihar Jigawa
- Aƙalla mutane uku ne suka rasu a wani sabon rikicin manoma da makiyaya a Jihar Nasarawa
- Jam’iyyar PDP ta sanar da ɗage babban taron shugabaninta na ƙasa
- Ƙungiyar Tuntuɓa ta Dattawan Arewa ta dakatar da shugaban majalisar ƙolinta
- Za’a dauki matakin kafa ‘yan sandan jihohi a Najeriya
Gwamnan yace za a mayar da dokar cin zarafin bil’adama zuwa majalisar dokokin jihar, domin tabbatar da an gyare-gyare a inda aka samu sabani.
Tunda farko, a jawabinta, ministar harkokin mata da cigaban yara, Pauline Tallen, ta bayyana fyade a matsayin abinda yafi kisan kai muni.