Gwamnan Jihar Anambra Mista Willie Obiano a jiya Litinin ya jagoranci zanga-zanga domin nuna adawa ga Kungiyar IPOB wanda suka bada umarnin a zauna a gida.

Gwamna Obiano, ya jagoranci zanga-zangar ne a babban birnin Awka na Jihar, bayan yan kasuwa sun ki fitowa domin su gudanar da kasuwancin su.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa dokar zaman gidan da yan Biafra suka kakaba a yankin yana neman daidaita tattalin arzikin jihar ta fuskar kasuwanci.

Manema Labaran da suka ziyarci babbar kasuwar Jihar, sun tabbatar da cewa duk da cewa an bude Kofar Kasuwar, amma masu shaguna sun ki fitowa.

Bayan gwamnan jihar ya shiga lamarin wasu yan kasuwar sun sake bude shagunan su.

Lamuran kasuwanci a yankin kudu maso gabashin Najeriya suna cigaba da fuskantar tasgaro a jiya Litinin.

A jihar Imo kuma, wasu yan kungiyar ta Biafra ne sun kori Daliban da suke rubuta Jarabawar WAEC.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: