

- Gwamna Zulum ya raba wa likitoci fiye da 80 didaje da kudi Naira miliyan 79 don inganta rayuwarsu - July 2, 2022
- Manyan Sarakunan kasar Yarabawa sunyi kiran samun zaman lafiya daga gwamnati kafin zaben 2023 - July 2, 2022
- Kasar Jamus za ta fara dawo wa da Najeriya dubban kayayyakin tarihin ta da aka wawushe tun lokacin mulkin mallaka - July 2, 2022
Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed ya yi alkawarin samar da ofishin ‘yan sanda cikin gaggawa a yankin Yelwan da ke karamar hukumar Bauchi.
Gwamnan ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da yake duba irin barnar da tashe-tashen hankulan suka haifar, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka uku, da lalata gidaje da dukiyoyi a yankin.
Ya kuma yi alkawarin sayo motocin aiki ga ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro domin kara kaimi, don tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Ya kuma umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) da ta yi lissafin dukiyoyin da aka lalata don baiwa gwamnati damar samar musu da kayayyakin agaji.
A nasa bangaren, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Umar Sanda, ya ce ‘yan sandan sun fara gudanar da cikakken bincike don gano musabbabin faruwar lamarin nan take da nufin gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aikar.