

- Mataimakin Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, shine ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar APC - May 27, 2022
- Shugaba Buhari yace gwamnatinsa tana assasa ginshiki mai inganci na kyakykyawar rayuwa domin yara manyan gobe a Najeriya - May 27, 2022
- Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta haramta bangar siyasa da tare da yin amfani da duk wani makami ga yaran yan siyasa - May 27, 2022
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ce samun cin gashin kai na iya zama da wahala kasancewar ‘yan kabilar Igbo ne suka mallaki rabin kasarnan.
Bala Mohammed, wanda dan takarar shugaban kasa ne a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ya bayyana haka a yau a lokacin da yake kokarin jawo hankalin wakilan jihar Anambra.
Yace idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa zai yi tafiya tare da nagartattun ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da kabila da addini ba.
Bala Mohammed ya ce matsalolin Najeriya sun ta’allaka ne kan nadin shugabannin, yana mai cewa idan shugabanci ya kasance mai gaskiya da adalci, kasar za ta gyaru.
Yace ya fi yin mu’amala da ‘yan kabilar Igbo kuma ya amfana da su, inda ya ce yawancin wadanda yake koyi da su ‘yan kabilar Igbo ne.
A cewarsa, harkokin kasuwanci a Kudu maso Gabas wata babbar dama ce da kowa ya kamata ya yi amfani da ita wajen bunkasa bangaren masana’antun wannan kasa.