Gwamnan jihar Bauchi ya yi zargin cewa masu aikata miyagun laifuka suna hada kai da wasu sarakunan gargajiya da jam’ian tsaro

0 57

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya yi zargin cewa masu aikata miyagun laifuka suna hada kai da wasu sarakunan gargajiya da baragurbin jami’an tsaro don haifar da tashin hankali kan mutanen jihar.

Gwamna Bala Mohammed, wanda ya bayyana hakan yayin taron majalisar kwamishinonin jihar a Bauchi, ya koka kan cewa lamarin ya sanya kokarin magance rashin tsaro ya zama mai wahala.

A saboda haka, gwamnan ya umurci kwamishinoninsa da sauran mataimakansa da su yi aiki kafada da kafada da shugabannin kananan hukumominsu a jihar don inganta tsaro a yankunansu.

Ya ce jihar Bauchi ta kasance daya daga cikin jahohin da suka fi zaman lafiya a Arewa maso Gabas.

A halin da ake ciki, gwamnatin jihar ta soke dukkan filayen da aka bayar a wuraren killace namun daji a jihar, sakamakon ayyukan ‘yan fashin daji a wuraren.

Leave a Reply

%d bloggers like this: