Gwamnan jihar Binuwai ya umarci mazauna jihar da su kare kansu daga hare-haren yan bindiga

0 62

Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya shaidawa mazauna jihar da su kare kansu bayan da gwamnatin jihar ta ce wasu da ake zargin makiyaya ne sun kashe mutane da dama yayin da suka kai hari a kauyukan manoma a kananan hukumomi uku na jihar.

Samuel Ortom ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da ya fitar jiya ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Nathaniel Ikyur.

Kakakin gwamnan ya kara da cewa, a wani kauyen karamar hukumar Gwer ta Yamma da ke jihar, wasu ‘yan bindiga da ya ce makiyaya ne sun kai wa al’ummar kauyen hari inda suka kashe mutane da dama.

Jihar Benuwe ta kasance jihar da ke fama da rikicin makiyaya da manoma tsawon shekaru da dama, inda aka yi asarar daruruwan rayukan mutane, tare da lalata wasu kauyuka da gonakin noma.

A shekarar 2017 ne Gwamna Ortom ya rattaba hannu kan dokar hana kiwo a sarari da nufin kawo karshen rikicin da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a jihar amma har yanzu ba a dena rikicin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: