Gwamnan Jihar Imo Mista Hope Uzodimma, ya bayyana cewa babu wani dalili da zai saka baza’a sake zabar Jam’iyar APC ba a shekarar 2023, biyo bayan yadda gwamnati mai ci take gudanar da ayyukan raya kasa.

Gwamna Uzodinma, ya bayyana hakan ne a fadar shugaban kasa a jiya bayan ya gana da shugaba Muhammadu Buhari a fadar sa dake Abuja.

A cewarsa, Jam’iyar APC ta samu gagarumar Nasara a cigaba da aikin rijistar yayan Jam’iya da aka gudanar kwanan nan.

Haka kuma ya ce Jagororin Jam’iyar APC ne suke da ikon kalubalantar Nasarar Farfesa Chukwuma Soludo, a matsayin wanda ya samu nasara a zaben gwamnan Jihar Anambra.

Mista Uzodimma, wanda shine shugaban Kwamatin yakin neman zaben Gwamnan Jihar Anambra, ya ce duk da cewa shugaba Buhari ya taya Soludo murnar samun nasarar cin zabe, hakan bazai hana Jam’iyar ta dauki matakin shari’a ba.

Kazalika, ya ce manufar kawowa shugaba Buhari ziyara shine domin su tattauna batutuwan da suke yankin kudu maso gabashin kasar nan ta fuskar tsaro.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: