Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya ce a tarihin Najeriya babu wata gwamnati da ta samu nasarorin da jam’iyyar APC ta samu

0 151

Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya ce a tarihin Najeriya babu wata gwamnati da ta samu nasarorin da jam’iyyar APC ta samu.

Gwamna Badaru ya bayyana haka ne a yau a wajen bikin kaddamar da jagororin jihohi 36 na kungiyar Jakadun jam’iyyar APC masu kula da shugabanci nagari da aka gudanar a Abuja.

Gwamnan jihar Jigawa ya samu wakilcin babban daraktan hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA) Kashifu Inuwa Abdullahi.

Gwamnan ya yi ikirarin cewa gwamnatin APC ta samu nasarori da dama a cikin shekaru bakwai da suka gabata a karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari amma ba’a yada nasarorin a kafafen sadarwa kamar yadda ya kamata.

Gwamna Badaru, ya bukaci kungiyar Jakadun jam’iyyar APC masu kula da shugabanci nagari da su hada kai wajen bayyana nasarorin da jam’iyyar APC mai mulki ta samu a fadin kananan hukumomin kasar nan 774 a daidai lokacin da zaben 2023 ke kara karatowa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: