Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Uba Sani, ya zargi wasu tsofaffin gwamnonin yankin Arewa maso Yamma da cin dunduniyar kawancen tsaro a tsakanin jihohin yankin ta hanyar yin mu‘amala da ‘yan fashin daji da ‘yan ta’adda.
Uba Sani, wanda bai ambaci sunaye ba, ya yi ikirarin cewa wasu gwamnonin sun dauki hanyar da ba ta dace ba wajen tafiyar da harkokin cikin gida na jihohinsu, wanda hakan ya janyo matsalar tsaro da ake fuskanta a halin yanzu.
Gwamnan ya kuma ce, samar da ‘yan sandan jihohi, wacca ita ce hanya daya tilo da za a kawo karshen kalubalen tsaro a Najeriya, inda ya ce hakan ya zama dole idan aka yi la’akari da karancin ikon da gwamnoni ke da shi a kan hukumomin tsaro.
Yace ya ji dadin yadda kusan dukkan gwamnonin jihohi a yanzu suka yarda cewa ‘yan sandan jihohi na da muhimmanci.
Uba Sani ya kuma yi fatan majalisar kasa ta 10 za ta sake duba batun ‘yan sandan jihohi, inda ya kara da cewa ko a matsayinsa na gwamna zai goyi bayan majalisar dokokin jihar akan hakan.