Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya fara rusa wasu gine-gine da ake kyautata zaton an gina su ba bisa ka’ida ba kan kadarorin gwamnati.
An tattaro cewa da yammacin jiya Juma’a ne tawagar da gwamnan ya kafa ta fara rusa wasu gine-gine da aka gina a cikin filin sukuwa a Kano.
Idan dai za a iya tunawa, Abba Kabir a jawabinsa na kaddamarwa a ranar Litinin ya ba da umarnin gudanar da tattaki ga hukumomin tsaro a jihar da su gaggauta karbe duk wasu kadarorin gwamnati da gwamnatin tsohon Gwamna Umaru Ganduje ta siyar. Wasu daga cikin kadarorin da gwamnan ke magana a kai sun hada da filaye a makarantu da kewaye, wuraren addini da al’adu, asibitoci, makabartu da wuraren kore, da kuma gefen katangar birnin Kano.