Gwamnan jihar katsina ya haramta bude dukkanin wajen sana’ar cajin waya a fadar jihar

0 77

Gwamnan jihar katsaina, Aminu Bello Masari ya haramta bude dukkanin wajen sana’ar cajin waya a fadar jihar, a kokarin magance matsalar tsaro da ya addabi jihar.

Gwamnan, ya bayyana haramcin hakan a fadar gwamnatin jihar a jiya litinin, yayin da yake kaddamar da shugabannin  kwamitin da zai ke duba akan wannan Sabuwar dokar.

Masari, ya gamsu da cewa wannan matakin da aka dauka, tare da na gwamnatin tarayya na katse layun Sadarwa zai taimaka matuka wajen rage ayyukan yan bingida a arewa maso yammacin kasar nan.

Kana-nan hukumomin da lamarin tsaron yafi kamari a jihar ta katsina sune, Batsari, Safana, Danmusa, Paskari, Sabuwa, Kurfi, Danja, Kaita, da Bakori, Funtua, Kankara, Musawa, sauran sune  Matazu, Dutsima, Mai’adua, Malumfashi da kuma Funtua.

Gwamna Masari  ya ce gwamnatin jihar zata ci gaba da nazarin hanyoyiin magance matsalar tsaro da daukar matakan yaki da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: