Gwamnan jihar Katsina ya nemi Alhazan jihar da suyi addu’ar Allah Ya yaye mata matsalar rashin tsaro

0 112

Gwamnan Jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda ya yi Kira ga alhazan Jihar Katsina da su yi amfani da sauran kwanakin da suka rage musu a Makkah wajen yi wa jihar addu’ar Allah Ya yaye mata ta’addancin da ke damun ta da ma ƙasa baki ɗaya.

Gwamnan ga yi wannan kira ne a lokacin da ya ziyarci shemomin alhazai na Jihar katsina a Minna.

Mallam Radda wanda ya zagaya dukkan shemomin na maza da na mata ya yi kira gare su da su ci gaba da yin dawafi domin rokon Allah Ya kawo wa jihar da Nijeriya zaman lafiya, sannan su yinwa kan su addu’ar samun nasara a rayuwa.

Gwamnan ya kuma nuna jin dadin sa wajen yadda ya sami alhazan a shemomin su cikin koshin lafiya.

Ya kuma yabd wa Hukumar Alhazai ta jihar Katsina kan yadda suka gudanar da aikin hidimar alhazai a Hajjin bana, inda ya ƙara da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da bata duk wani tallafi da take nema.

Share

Leave a Reply

%d bloggers like this: