Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya sanar cewa shi ne Mukaddashin Shugaban Rikon Jam’iyyar APC na Kasa

0 77

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya sanar cewa shi ne Mukaddashin Shugaban Rikon Jam’iyyar APC na Kasa.

Gwamnan ya bayyana haka ne a hedikwatar Jam’iyyar a yau Litinin, bayan wasu rahotanni da ke cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sallami Shugaban Rikon Jam’iyyar na Kasa kuma Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, daga mukamin.

Da yake magana bayan taron da ya jagoranta na Kwamitin Rikon Jam’iyyar na Kasa da shugabanninta na jihohi, Gwamna Bello ya ce, Shugabannin Jam’iyyar na Jihohi sun karbi rantsuwar mika wuya.

Ya ce, sun tattauna inda aka kwana a shirin babban taron Jam’iyya da abin da ya kamata a yi nan gaba domin gudanar da taron na ranar 26 ga watan Maris cikin nasara.

An tambaye shi dalilin da ya jagoranci taron, sai ya ce, shi ne Mukaddashin Shugaba, kuma ya dan jima yana aiki a matsayin riko bayan Gwamna Mai Mala Buni ya yi tafiya.

Da aka tambaye shi game da gaskiyar batun sallamar Buni daga kujerar, Gwamna Abubakar Sani Bello ya ce, ba shi da ta cewa.

Dambarwar sallamar na zuwa ne a yayin da Buni ke duba lafiyarsa a kasar Jamus, kuma washegarin tafiyar Buhari kasar Birtaniya domin ganin likita.

Leave a Reply

%d bloggers like this: