Labarai

Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike ya ce hanya daya da zata kawo karshen hare-haren yan bindiga ita ce korar gwamnatin Jam’iyar APC

Gwamnan Jihar Rivers kuma Dan Takarar Shugaban Kasa a Jam’iyar PDP Nyesom Wike, ya ce hanya daya ce ta kawo karshen hare-haren yan bindiga, ita ce korar gwamnatin Jam’iyar APC daga kan Mulki tare da zabar Jam’iyar PDP a shekarar 2023.

Gwamna Wike ya bayyana hakan ne a birnin Jos na Jihar Plateau a lokacin da yake yiwa Delegates din PDP Jawabi.

Wike ya bukaci mutanen Jihar su fito kwansu da kwarkwata wajen ganin cewa Jam’iyar PDP ta karbi ragamar Mulki a Jihar da kuma Kasa baki daya a shekarar 2023.

Haka kuma ya ce yazo Jihar ne domin ya fada musu aniyar sa ta tsayawa takarar shugaban kasa, inda ya ce shi kadai ne dan takarar da yake da nagartar fitar da kasar nan daga cikin halin da Jam’iyar APC ta jefa yan Najeriya.

Tun farko a Jawabinsa, Shugaban Jam’iyar PDP na Jihar Plateau Hon Chris Adukuchili Hassan, ya bayyana Wike a matsayin aminin Jihar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: