Gwamnan jihar Rivers ya gargadi tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan kan kada ya koma jam’iyar APC

0 79

Gwamnan Jihar Rivers Mista Nyesom Wike, ya gargadi tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan kan kada ya koma Jam’iyar APC mai mulki.

Da yake zantawa da gidan BBC Pidgin Gwamnan ya ce Jam’iyar APC zata rushe sauran mutuncin da tsohon shugaban Kasar yake dashi matukar ya shiga Jam’iyar.

Mista Wike ya bukaci Goodluck Jonathan ya ci gabata da zama a Jam’iyar PDP matukar yana sha’awar sake tsayawa Takarar shugaban Kasa a 2023.

A cewarsa, yan Najeriya na cigaba da yaba masa fiye da gwamnatin Shugaba Buhari, wanda ta dauki Alkawarirrika kuma ta kasa cikawa.

A shekarar 2015 ne Shugaba Buhari ya kada Shugaba Goodluck Jonathan, na Jam’iyar PDP bayan kada kuri’u.

Kawo yanzu tsohon shugaban Kasar bai bayyana aniyarsa ta sake neman Takara a shekarar 2023 ba. Sai dai Jam’iyar APC ta ce baza ta bashi Takara ba koda ya shigo Jam’iyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: