Gwamnan jihar Sokoto ya karɓi baƙuncin manyan jami’an tsaro wanda gwamnatin tarayya ta tura

0 106

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya karbi bakuncin manyan jamian tsaro wanda gwamnatin tarayya ta tura karkashin jagorancin, mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Major janar Babagana Munguno mai ritaya.

Gwamnan yayin da yake zantawa da wakilan gwamnatin tarayyar dangane da yanayin da jihar ciki, ya bayyana irin da kalubalen yan bindigar ke fuskantar daga jamian rundunar operation Hadarin Daji a jihar Zamfara, wanda acewarsa shine ya sanya yan bindigar sauka kwararo izuwa jihar Sokoto, suke kaddamar da ayyukansu ido na ganai ido musamman a yankunan Isa, da Sabon Birni, Tangaza, Illela da sauran wasu kananan hakumomi a jihar.

Gwamna Tambuwal yace a matsayinsa na mataimakin shugaban kungiyar gwamanonin arewacin kasar nan yace yana da masaniya kan kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen yaki da ayyukan taaddanci a fadin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: