Labarai

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya sha alwashin tallafawa matasa 300,000 ta hanyar basu Jari domin bunkasa Kasuwancin su

Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya sha Alwashin tallafawa Matasa dubu 300,000 ta hanyar basu Jari domin bunkasa Kasuwancin su a wani mataki na dakile Talauci a Jihar.

Gwama Buni ya bayyana hakan ne a lokacin da magoya bayan sa suka shirya masa wani gangami domin karramashi bayan da ya dawo Jihar, sakamakon shugabantar APC na rikon kwarya tsawon shekaru 2.

Da yake jawabi ga Daruruwan Magoya baya a filin taro na August Stadium a Damaturu, Gwamna Buni ya yi Alkawarin raba Babura masu kafa 3 ga Matasan da suke Jihar domin mayar dasu masu Dogaro da kansu.

Gwamnan ya yi tulawar nasarorin da ya samu a lokacin da yake shugabantar Jam’iyar APC a matakin Kasa, inda ya gode musu bisa Addu’oin su gareshi.

Kazalika, ya yi kira ga yan Siyasar Jihar su rika kyautatawa yan Jam’iyar, inda ya ce Marowatan yan Siyasa basu da hurumi a gwamnatin sa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: