Labarai

Gwamnan jihar Yobe ya amince da kara shekarun ritayar malaman makaranta daga aiki daga 60 zuwa 65 da kuma dadewa a aiki daga shekara 35 zuwa 40

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da kara shekarun ritayar malaman makaranta daga aiki, daga shekara 60 zuwa 65 da kuma dadewa a aiki daga shekara 35 zuwa 40, duk wanda ya fara zuwa a farko.

Jami’in yada labarai a ofishin shugaban ma’aikatan jihar Yobe, Alhassan Sule-Mamudo, ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Damaturu, babban birnin jihar.

Sai dai, sanarwar ta yi nuni da cewa babu tabbacin cin gajiyar karin shekarun ritayar kai tsaye, inda tace za a gwada lafiyar malaman makarantar domin tabbatar da cancantarsu.

Ya kara da cewa wadanda aka samu sun tsufa dayawa ko basu da koshin lafiya sosai, za a basu shawarar ajiye aiki.

An raiwato cewa jihar Yobe na cikin jihoshin kasarnan da ake aiwatar da shekarun barin aiki kala biyu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: