Gwamnan jihar Zamfara ya kaddamar da babban asibitin kwanciya mai gadaje 300 a karamar hukumar Birnin-Magaji

0 67

Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara a yau ya kaddamar da babban asibitin kwanciya mai gadaje 300 a karamar hukumar Birnin-Magaji ta jihar.

Gwamna Matawalle, wanda Shugaban Kwamitin Kula da Asibitin, Dr Bashir Maru ya wakilta, ya sanar da hakan ga manema labarai.

Ya ce gwamnatin jihar za ta dauki karin ma’aikata don samar da isassun ma’aikata a asibitocin jihar ta Zamfara.

Gwamnatin tsohon Gwamna Abdullaziz Yari ce ta fara aikin kuma ta aiwatar da kashi 40 cikin 100 na aikin kafin wa’adinta ya kare.

Gwamnatin Matawalle ta karbi aikin kuma ta kammala ginin babban asibitin kashi da 60 cikin dari.

Babban likitan asibitin, Dakta Salisu Ya’u, ya ce ayyukan asibitin gaba daya za su tashi daga ginin wucin gadi zuwa sabon ginin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: