Gwamnati ta bukaci mazauna Legas da su kwantar da hankalinsu biyo bayan ambaliyar ruwan sama a birnin

0 208

Gwamnatin jihar Legas ta bukaci mazauna garin da su kwantar da hankalinsu biyo bayan ruwan sama da aka shafe sa’o’i tara anayi ba tare da kakkautawa ba, wanda ya haifar da ambaliya a fadin birnin.

Kwamishinan  Muhalli na Jihar Legas, Tokunbo Wahab, ya yi cikakken bayani kan lamarin tare da bawa jama’a tabbacin daukar matakin gaggawa domin dakile ambaliyar.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka fara tun da sanyin safiyar jiya Larabar, wanda kuma ke ci gaba da yi tun a makon da ya gabata, lamarin da ya haifar da ambaliya.

An shawarci mazauna yankunan karkara da su ƙaura zuwa manyan filaye don kare rayukansu da dukiyoyinsu. A ci gaba da kokarin da ake na dakile afkuwar irin haka, gwamnatin jihar ta kaddamar da shirin kula da magudanan ruwa na tsawon shekara guda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: