Gwamnati ta yi amfani da dajin Sambisa wajen ayyukan noma – Sheikh Ayara

0 268

Shugaban kungiyar Hijira ta kasa, Farfesa Badmus Olarenwaju Yusuf, ya yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya magance hauhawar farashin kayayyakin abinci da sauran kayayyaki a kasar.

Da yake jawabi yayin bikin sabuwar shekarar Hijira ta 1445 da aka gudanar a birnin Ilọrin, Badmus ya ce lamarin ya durkusar da jin dadin zamantakewa da ci gaban al’umma.

Yusuf ya kuma yi kira ga musulmi da su lura da makircin da kasashen yamma ke kullawo na cin zarafin Al-Qur’ani mai girma da kuma yunkurin bata sunan addinin Musulunci.

A sakonsa a wajen taron, wakilin kungiyar Ansarul Islam ta kasa, Sheikh Abdulmumin Aara, ya yi kira ga Tinubu da ya magance illar karin farashin man fetur ga talakawan kasar nan. Ya shawarci gwamnati da ta yi amfani da dajin Sambisa da ke Maiduguri a jihar Borno, wajen ayyukan noma domin dakile ayyukan tada kayar baya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: