Gwamnatin ƙasar Uganda na daf da rasa babban filin jirgin samanta ga ƙasar China saboda gaza biyan bashi

0 192

Gwamnatin kasar Uganda na daf da rasa babban filin jirgin samanta ga kasar China saboda gaza biyan bashin da aka ba ta.

Gwamnati ta gaza canja yarjejeniyar bashin da Chinan wacce ke da sharuddan biyan da ya hada da tashar jirgin samanta daya tilo.

An shigar da filin jirgin saman kasa da kasa na Entebbe da sauran kadarorin kasar Uganda tare da amincewa masu bayar da bashi na China za su karba bayan kasa biyan bashin.

Rahotanni sun ce, shugaba Yoweri Museveni ya aike da tawaga zuwa birnin Beijing na kasar China da fatan sake tattaunawa kan sharuddan masu Tsauri.

Ziyarar dai ba ta yi nasara ba saboda hukumomin China sun ki bayar da damar yin wani sauyi a ka’idojin yarjejeniyar.

Kin amincewa da rokon da Uganda ta yi na sake tattaunawa kan sharuddan masu tsauri na rancen shekarar 2015 ya bar gwamnatin Museveni cikin rudani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: