Gwamnatin Amurka ta ce za ta taimakawa Najeriya a yakin da take yi da ‘yan fashin daji

0 122

Gwamnatin Amurka ta ce za ta taimakawa Najeriya a yakin da take yi da ‘yan fashin daji.

Mataimakin babban mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar Amurka, Jon Finer, ya ba da wannan tabbacin jiya yayin ganawa da manema labarai a Abuja.

A halin da ake ciki, a jiya sojojin Najeriya sun kashe mayakan ISWAP akalla 16 a karamar hukumar Jere ta jihar Borno.

Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa sojojin sun kashe masu tayar da kayar baya yayin da suke fatattakar harin da kungiyar ta ISWAP ta kaddamar a yankin Chabbal dake yankin.

Maharan sun shiga garin ne ta cikin garin Mafa cikin manyan motocin bindigogi a yammacin jiya.

Mayakan na ISWAP sun fara harbin kan mai uwa da wabi, bayan sun mamaye garin.

Daya daga cikin majiyoyin wanda jami’in leken asirin soji ne, ya shaidawa PRNigeria cewa nan take sojojin bataliya ta 2I2 da na bataliya ta 195 dake Jere suka bazama aiki, inda suka kashe mayaka 16.

Leave a Reply

%d bloggers like this: