Gwamnatin Amurka tayi kira ga kasashen Afirka su mayar da martani mai tsauri akan mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine

0 110

Gwamnatin Amurka a jiya tayi kira ga kasashen Afirka su mayar da martani mai tsauri akan mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine.

Jami’an diplomasiyyar Amurka sun zanta da manema labarai a Dakar, babban birnin kasar Senegal.

Sun tsara yadda zasu taimaka wajen dakile illar tattalin arzikin da rikicin na Ukraine zai jawowa kasashen Afirka.

Wani jami’in ofishin harkokin Afrika na Amurka, ya isa kasar Senagal domin tattaunawa da mutane, ciki har da shugaban kasar Macky Sall, wanda a yanzu shine yake rike da mukamin shugaban kungiyar tarayyar Afrika.

Ziyarar na zuwa ne bayan mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine yake raba kan kasashen Afrika.

Kimanin rabin kasashen Afrika ne suka ki kada kuri’a akan bukatu biyu na majalisar dinkin duniya, dake neman kawo karshen mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine.

Najeriya ta goyi bayan dukkanin bukatun.

Leave a Reply

%d bloggers like this: