Gwamnatin Angola ta dakatar da Albashin Likitoci fiye da dubu 5,000 biyo bayan tafiya yajin aiki, ba bisa ka’ida ba

0 80

Gwamnatin Angola ta dakatar da Albashin Likitoci fiye da dubu 5,000 biyo bayan tafiya yajin aiki, ba bisa ka’ida ba.

Kungiyar Likitocin Angola ta fara yajin aikin gamagari a makon da ya gabata saboda kudurin su na bukatar karin Albashi da kuma yanayin aiki.

Yajin aikin ya jefa yanayin lafiyar kasar cikin wani hali, duk da cewa akwai likitocin da suke yin aikin bada agajin gaggawa.

Likitocin sun ce rashin kyawun Albashin da rashin kayan aiki a Asibitoci na daga cikin Dalilan da suka sanya su tafiya yajin aikin.

Yajin aikin de shine karo na biyu cikin watanni 4 a kasar, domin ko a watan Disambar 2021 Likitocin sun shiga yajin aikin sakamakon mutuwar Yara 20 a Asibitin birnin Luanda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: