Gwamnatin Donald Trump na ci gaba da ƙoƙarin mayar da ‘yan gudun hijira zuwa wasu ƙasashe uku, duk da ƙalubalen shari’a da ke hana hakan a halin yanzu.
Wata kotu a Amurka ta yanke hukuncin cewa tilas ne a ba waɗanda aka kama damar kare kansu a kotu kafin a kore su daga ƙasar, matakin da ke rage ƙarfin aiwatar da tsare-tsaren gwamnatin Trump.
A gefe guda kuma, gwamnatocin Libya da ke fafatawa da juna sun ce ba za su amince da karɓar waɗanda aka kora ba, musamman duba da irin cin zarafin da masu neman mafaka ke fuskanta a ƙasar.
Rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya na 2024 data gabata ya bayyana cewa an sami shaidu na aikata laifukan cin zarafin bil adama, ciki har da gano ƙaburbura masu ɗauke da gawawwakin ‘yan gudun hijira, da kuma nutsewar dubban mutane a yunkurin tserewa daga ƙasar zuwa Turai.