Gwamnatin Jigawa Ta Kulla Yarjejeniya Da Kasar Holland Kan Yaki Da Iftila’in Ambaliyar Ruwa

0 76

Gwamnatin jihar Jigawa ta kulla yarjejeniya da kasar Holland kan yaki da iftila’in ambaliyar ruwa dake addabar jihar kowace shekara.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan ayyuka na musamman Auwalu Danladi Sankara ya fitar jiya a Dutse, inda ya ce an gudanar da bikin sanya hannun a ofishin jakadancin Najeriya dake birnin Hague a kasar ta Holland inda gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya sanya hannu a madadin gwamnatin jihar.

Sanarwar ta bayyana cewa, yarjejeniyar ta fahimtar juna da aka kulla da kwararrun masana harkar magance ambaliyar ruwa na kasar Holland da gwamnatin jihar Jigawa na da nufin ganin an kawo karshen ambaliyar ruwar da ta addabi jihar a duk shekara tare da salwantar da rayukan mutane da dabbobi da kuma kawo tsaiko ga harkokin tattalin arziki.

A cewar sanarwar, a lokacin da yake rattaba hannu kan yarjejeniyar ta fahimtar juna, Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana fatansa na ganin cewa hadin gwiwa da kwararrun ‘yan kasar Holland zai samar da mafita ta karshe wajen kawo karshen ambaliyar ruwa a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: