Gwamnatin Jihar Bauchi ta fitar da Naira Miliyan 779 da Dubu 700 domin gyara Sakatariyar Mulki ta Jihar.

Shugaban Ma’aikata na Jihar Bauchi Malam Yahuza Ningi, shine ya bayyana hakan ga manema labarai jiya a Bauchi.

A cewarsa, gyaran Sakatariyar na daga cikin kudurin gwamnatin na samar da kyakkyawan yanayin aiki ga Ma’aikatan gwamnati domin kyautata kwazon su.

Haka kuma ya ce Sakatariyar wanda aka ginata a shekarar 1983 tana bukatar yin hakan biyo bayan sauye-sauyen zamani.

Mista Ningi ya ce an kasa aikin zuwa bangarori 3, wanda suka kunshi gina Kwalta a cikin harabar, gyaran tasawirar wutar lantarkin da kuma kewaye ta da gini.

Haka kuma ya ce gwamnati ta dauki kamfanin da zaiyi aiki tantance yan fansho da biyan garatuti.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: