Gwamnatin Jihar Borno ta haramta duk nau’ikan bangar siyasa da dabanci ko daukar makami ba bisa ka’ida ba.

Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ta ce duk wanda aka kama yana bangar siyasa ko ya dauki kowane irin makami ba tare da izini ba zai yaba wa aya zaki.

Kwamishinan Wasanni da Harkokin Matasa da kuma Samar da Ayyukan Dogaro da Kai na jihar, Malam Sa’inna Buba, ya ce Gwamna Zulum ba zai lamunci duk wani rikici ba da matasa ke yi da sunan dabanci ko bangar siyasa.

A cewarsa, kafin fitar da sanarwar sai da Gwamna Zulum, tare da Kwamishinan ’Yan Sanda da Darakan hukumar DSS da Kwamandan hukumar Sibil Difens na jihar suka yi zama da shugabannin matasa.

A cewarsa, Gwamna Zulum ba zai daina biyan alawus ga matasan jihar marasa aikin yi ba wanda ya fara shekara biyu da suka gabata.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: