Gwamnatin Jihar Gombe tace za ta dauki matasa sama da dubu 2 domin aikin tsaro, kula da zirga-zirgar ababen hawa da gyaran muhalli.

Shugaban hukumar tsaro, kula da zirga-zirgar ababen hawa da gyaran muhalli ta jihar Gombe, Barrista Sani Ahmed, ya sanar da haka a jiya wajen rantsar da matasa 500 da aka dauka domin shirin a sansanin horas da matasa masu yiwa kasa hidima NYSC a yankin karamar hukumar Akko ta jihar.

Yace ma’aikatan hukumar zasu kasance masu kula da zirga-zirgar ababen hawa da mutane da kuma dabbobi, tare da tallafawa hukumomin tsaro wajen tsaftace jihar.

Sani Ahmed, wanda kuma shine mai bawa gwamnan jihar shawara akan cigaban rayuwar jama’a, ya kara da cewa shirin wani bangare ne na shirye-shiryen daukar matasa dubu 20 da suka kammala karatu aiki.

Gwamnan jihar, Inuwa Yahaya, ya nanata jajircewarsa wajen dakile matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa ta hanyar sama musu da jari da koya musu sana’o’i domin dogaro da kai.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: