Gwamnatin jihar Gombe ta fara binciken man fetur a jihar

0 89

Gwamnatin jihar Gombe ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tare da wani kamfanin mai da iskar gas mai suna Rift Oil, domin binciken albarkatun man fetur a jihar.

Gwamnan jihar Inuwa Yahaya, wanda ya jagoranci bikin rattaba hannu a jiya, ya ce fiye da kowane lokaci, bukatar fitar da mai da iskar gas da aka gano a yankin Kolmani, ya zama dole.

Ya ce tare da sanya hannu kan Dokar Masana’antar Man Fetur da cece-kucen da wasu jihohi ke yi don tattarawa da rike Harajin VAT, sabon tsarin zai taimaka sosai ga shirin inganta samar da kudaden shiga na gwamnatinsa.

Matakin da jihar ta dauka ya biyo bayan rashin jituwa tsakanin hukumar tara haraji ta tarayya da wasu gwamnoni daga kudancin kasarnan kan hakkin karbar harajin VAT.

Inuwa Yahaya ya ce akwai makamashin hydrocarbon dayawa a yankin Kolmani da sauran makamashi daban-daban.

Leave a Reply

%d bloggers like this: