Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da dokar kafa Hukumar Kula da makarantun Tsangaya

0 146

A jahar Jigawa a wani mataki na hana barace-barace da kuma kawo sauyi daidai da zamani a makarantun tsayar jahar, majalisar dokokin jihar ta amince da dokar kafa Hukumar Kula da makarantun Tsangaya biyo bayan gabatar da rahoton kwamatin Ilimi matakin farko da shugaban kwamatin Hon. Ado Yakubu Zandam yayi a zaman majalisar dokokin jahar na jiya.

Yayin tattaunawar sa da wakilin mu na Dutse Zulkiflu Abdullah Dagu bayan kammala zaman majalisar, Hon. Ado Yakubu ya shaida masa cewar da zarar gwamnan jahar ta sanya wa dokar hannu za’a fara gina makarantun tsangayar guda uku-uku a kowacce shiyya dake jahar a matakin gwaji kafin a faɗaɗawa daga baya.

Ga ƙarin bayanin da yayiwa wakilin namu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: