Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Bada Ayyukan Tituna Sama Da 100 A Cikin Shekaru Takwas Da Suka Gabata

0 62

Gwamnatin jihar Jigawa ta bada ayyukan tituna sama da 100 a cikin shekaru takwas da suka gabata.

Babban sakataren ma’aikatar ayyuka da sufuri Injiniya Datti Ahmed ya bayyana hakan a wajen kaddamar da aikin titin Kwanar Garki zuwa Albasu zuwa Jigawar Dan-Ali wanda gwamnatin mai ci ta sake ginawa.

Haka kuma an kaddamar da titunan cikin garin Jigawar Dan-Ali a karamar hukumar Babura.

Babban sakataren ya bayyana cewa gwamnati mai ci ta gaji ayyukan tituna 42 daga tsohuwar gwamnati inda ta kammala 40.

Hakazalika Gwamnan ya kaddamar da babban asibitin Garki mai gadaje 100 da gwamnatin jihar ta gina tare da samar da kayan aiki. Da yake jawabi Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana cewa hakan na daga cikin kokarin gwamnatin sa na samar da ababen more rayuwa ga al’ummar jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: