Gwamnatin jihar Jigawa ta biya Naira biliyan 9 da miliyan 409 ga yan fansho

0 127

Asusun Adashen Gata na fansho na Jiha da kuma Kananan Hukumomin Jihar Jigawa ya biya Naira Biliyan 9 da Miliyan 409 ga Ma’aikata dubu 12,627 wanda suka yi ritaya a shekarar 2021.

Sakataren zartarwa na Asusun Alhaji Kamilu Aliyu Musa shine ya sanar da hakan a lokacin kaddamar da biyan hakkokin ma’aikatan a pension house, inda ya ce daga watan Janeru zuwa Disambar wannan shekara kimanin Naira Biliyan 9 da Miliyan 400 ne suka raba ga Ma’aikata dubu 12 da 627 da suka yi ritaya.

A cewarsa, kudaden sun hada da na Ma’aikatan da suka mutu suna bakin aiki, da suka karbi hakkin su na ritaya da kuma Fanshon Ma’aikatan a 2021.

Haka kuma ya ce Ma’aikatan sun hada da Ma’aikatan Jiha da na Kananan Hukumomi da kuma Fannin Ilimi na Kananan Hukumomi.

Kazalika, ya bada tabbacin cewa gwamnatin Jihar nan da kuma Hukumar zasu tabbatar da cewa sun kyautata rayuwar Ma’aikatan da suka yi ritaya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN ya rawaito cewa hukumar ta kaddamar da biyan kudi fiye da naira miliyan dari hudu da tamanin da uku a matsayin hakkokin ma’aikatan jiha da kananan hukumomi dana sashen ilmi su 209 da suka yi ritaya daga aiki a wannan watan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: