Gwamnatin jihar Jigawa ta dauki dalibai 104 aiki

0 70

Gwamnatin jihar Jigawa ta dauki dalibai 104 aiki wadanda suka samu sakamako mafi daraja na first class a jami’oin da suka kammala.

Kwamishinan ilmi na jiha Dr Lawan Yunusa Danzomo ya sanar da hakan ta wani shirin radio Jigawa.

Yace Gwamna Badaru Abubakar ne ya amince da daukar matasan aiki.

Yace bisa al’ada duk dalibin Jigawa daya kammala karatun digiri kuma ya sami sakamako mafi daraja za a bashi aiki kai tsaye.

Yunusa Danzomo ya kara da cewar a yanzu haka ana tantance karin takardun wasu daliban na Jigawa da suka samu sakamako mafi daraja a karatunsu na digiri.

Yace kashi 58.9 zuwa kaso 65.5 cikin 100 na daliban Jigawa ‘yan sikandare da suka rubuta jarabawar NECO ta bana, sun samu credit biyar zuwa sama, wanda zai basu damar samun guraben karatu a makarantun gaba da sakandire a fadin kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: