Gwamnatin jihar Jigawa ta fadada shirin kula da lafiyar masu karamin karfi a kyauta na gwamnatin tarayya zuwa kananan hukumomin jiharnan 27

0 72

Hukumar asusun kiwon lafiya ta jihar Jigawa ta fadada shirin kula da lafiyar masu karamin karfi a kyauta na gwamnatin tarayya zuwa kananan hukumomin jiharnan 27.

Sakataren zartarwar hukumar, Dr Nura Ibrahim, ya sanar da hakan ta cikin wani shirin radio Jigawa.

Yace a baya, ana gudanar da shirin ne a asibitoci 65 a kananan hukumomi 9 amma a yanzu an fadada shi zuwa asibitoci 279 a kananan hukumomin jiharnan 27.

Nura Ibrahim ya kara da cewa an kara yawan adadin masu amfana da shirin daga 157 a kowacce mazaba zuwa 161.

Yace hukumar ta yiwa dukkannin wadanda suke cikin shirin su fiye da dubu 46 katunan sheda wadanda za a raba musu.

Sakataren zartarwar hukumar yace har yanzu hukumar tana cigaba da yiwa ma’aikatan jiha da kananan hukumomi da na sashen ilmi rijistar shiga shirin bayar da magani daga ranar 1 ga wata zuwa 19 ga kowanne wata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: