Gwamnatin Jihar Jigawa tace ta gina sabbin makarantu da dama kari kan wadanda ake dasu a fadin jiharnan.

Mataimakin Gwamnan Jiha, Malam Umar Namadi ya bayyana haka lokacin bude bita ta kwanaki uku da aka shiryawa malaman turanci da lissafi kan dabarun aiki da na’urar kwamfuta a Dutse.

Umar Namadi wanda ya sami wakilcin shugaban ma’aikata na jiha, Hussaini Ali Kila, ya ce gwamnati tana bakin kokarin ta wajen bunkasa ilimi a kowane mataki.

A jawabinsa, shugaban hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA), Malam Kashifu Inuwa yace makasudin taron shine domin tallafawa harkokin koyo da koyarwa ta hanyar ba da horo ga masu ruwa da tsaki.

Da yake nasa jawabin kwamashinan ilimi na Jiha, Dokta Yunusa Lawan Danzomo ta bakin babbar sakatariyar ma’aikatar, Hajiya Safiya Muhammad, ya yabawa kungiyar hadakar kungiyoyin matasa na kasa bisa shirya taron bitar.

Tun farko a jawabinsa shugaban kungiyar, Comrade Aminu Aminu ya ce sun shirya taron bitar ne da hadin gwiwar hukumar NITDA domin cigaban harkokin ilimi a jiha.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: