Gwamnatin jihar Jigawa ta kafa makarantu guda 117 tare da dawo da dubban daliban makarantun kwana zuwa na jeka ka dawo

0 65

A wani bangare na kokarin gwamnatin jihar Jigawa da dakile rashin tsaro ga dalibai, gwamnati ta kafa makarantun sakandare na jeka ka dawo guda 117 tare da dawo da dubban daliban makarantun kwana zuwa na jeka ka dawo.

Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jiha, Dakta Lawan Yunusu Danzomo, ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Dutse.

Lawan Danzomo ya yi bayanin cewa manufar ita ce dakile duk wani shiri da yunkurin batagarin da ke sace daliban makaranta.

A cewarsa gwamnati ta kashe sama da naira miliyan dubu 20 don samar da kayayyakin koyo da koyarwa a makarantu sama da dubu 3, wadanda ke da dalibai sama da miliyan daya da rabi.

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati mai ci ta samu mafi girman kaso a kokarin habaka makarantu tare da dukkan mahimman kayayyakin koyo da koyarwa.

Lawan Danzomo ya cigaba da cewa sama da manyan mutane dubu 30 ne da ba sa zuwa makaranta suka shiga cibiyoyi 81 na hukumar ilimin manya da gwamnatin jihar ta samar a kananan hukumomi 27.

Leave a Reply

%d bloggers like this: